Kalmar “Allah”

Kalmar “Allah”
Kalmar “Allah” suna ne madaukaki na mahallici wanda wasu suka tafi a kan cewa shi ne suna mafi girma.
Allah yana da siffofi da ayyuka, wadannan siffofin nasa su ba irin na sauran samammu ba ne, domin shi siffofinsa azali ne wadanda suke tare da shi tun azal, amma sauran halittu siffofinsu suna bujuro musu ne.
Sai dai tun farko yana da kyau mu sani cewa sanin Allah madaukaki yana bukatar ayyana hanyar saninsa ga mai rubutu, domin wani yakan yi bayanin Sanin Ubangiji madaukaki ta hanyar Falsafa, wani kuma ta hanyar Irfani, da makamantansu. Amma mu a nan muna son yin wani gajeren bayani game da Allah madaukaki ta hanyar hankali da shara’a ne.
Da farko dai mu sani cewa Allah ya yi mana baiwar da babu wani mai rayuwar a doron kasa da ya same ta. Ya yi mana falalar da baiwar karfin tunani da kyautar hankali, don haka ne ma ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukaki yana cewa: “Zamu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya ne”. Surar Fussilat: 53. Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba”. (Surar Bakara: 170). Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116.
Wannan ni’imar ta hankali ita ce ta wajabta mana yin bincike domin sanin Allah madaukaki, ta yadda muna iya cewa dokokin hankali suna tilasta mana hakan. Don haka ne abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali.
Kuma babban kuskure ne ga wani mutum ya ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane, ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa, ya san ubangijinsa .
Don haka a kanmu akwai nauyin wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida, bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba, kuma na farko shi ne ubangiji madaukaki. Wannan wajabcin saninsa bai samo asali daga nassosin addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi.
Sau da yawa marubuta sukan kawo sunayen Allah da siffofinsa kamar haka: Allah madaukaki daya ne makadaici, babu wani abu kamarsa, magabaci ne, bai gushe ba kuma ba ya gushewa. Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani, kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu tamka gare Shi, sannan ba a iya riskarsa da wasu mariskai.
Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (a.s).
Mafi girman siffar da take fara zuwa a jerin sunayensa ita ce kadaitawa, domin ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, da samuwarsa, da siffofinsa da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan.
Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (s.w.t), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.
Wasu mutanen sun so su kore musulunci daga dukkan wanda yake ziyarar kaburbura, da tawassuli da waliyyan Allah, da da’awar cewa shirka ne. sai dai lamarin ba haka yake ba, domin ziyartar kaburbura da gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada. Wadannan ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (s.w.t) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa, da taimakon talaka.
Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (s.w.t) ko kuma shirka a bautarSa, haka nan sauran ayyukan ibada. Dukkan wadannan ayyukan ba komai ake nufi da su ba sai rayar da al’amuran Allah da waliyyansa, da sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “Wannan, duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.
Daya daga cikin mafi girman lamari a bahasin sanin Allah madaukaki shi ne na siffofinsa tsarakaka; da farko dai ana kasa wadannan siffofi zuwa siffofi tabbatattu na kamala da (jamal) kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa.
Wasu sun dauka wadannan siffofin su daban ne, kuma kari ne kan samuwar zatin Allah, ta yadda su ma suna da tasu samuwar ta daban. Sai dai mu muna cewa wadannan siffofi ba kari suke ba a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.
Amma wadannan siffofin sun sassaba a ma’anoni, ba a hakikanin samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar Ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga Ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.
Sannan akwai wasu siffofi masu nuna aikin ubangiji kamar  halittawa, arzutawa, gabatuwa, da kuma samarwa. Wadannan, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da ayyukansa ga bayinsa.
Amma siffofin da ake kira salbiyya wato korarru; da aka fi saninsu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore nakasa  daga ubangiji ko duk wata tawaya kamar jiki, sura, fuska, motsi, da rashin motsi, nauyi, da rashin nauyi, da sauransu.
Shugabanmu Amirul Muminin (a.s) ya yi nuni ga hakikanin siffofin Allah madaukaki yana mai cewa: Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi , saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin .
Daya daga cikin siffar Allah da aka yi ta ja-inja a kanta ita ce Adalcin Allah, amma mu a takaice a nan zamu ce: Duk wani nau’in zalunci ya koru ga Allah, domin dukkan hanyoyi hudu da za a iya yin zalunci sun koru daga gareshi kamar haka:
1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa zalunci ba ne.
2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma kasa barin aikata shi.
3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma kasa barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.
4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya kasance ya yi zalunci ne kawai don sha’awa da wasa.
Dukkan wadannan siffofi sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.
Sannan haka nan Allah ba ya tilasta wa bayi aikin da ba zasu iya yin sa ba, kamar yadda ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Babban nauyin da yake kan baligi shi ne wajabcin ya san Allah madaukaki, bai halatta ba ya bi wani a kan haka ba koda kuwa babansa ne, dole ya yarda Allah daya ne, ta yadda da babansa ko malaminsa zai ce Allah sabanin haka ne, to ba zai bi ba.
Cibiyar Al’adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Tuesday, April 13, 2010

Ƙara sabon ra'ayi