Siffofin Ubangiji
Siffofin Ubangiji (s.w.t)
Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai siffofi tabbatattu na hak'ik'anin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wad'anda suke su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da suke k'ari a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, k'udurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce k'udurarsa, Shi mai k'udura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai k'udura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.
Na’am siffofinsa sun sassaba a ma’anoninsu ne ba a hak'ik'aninsu da samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassab'a a samuwarsu, da an sami k'ididdigar Ubangiji, kuma da ba a sami kad'aitaka ta hak'ik'a ga Ubangiji ba, wannan kuwa ya sab'a wa Ak'idar Tauhidi.
Tabbatattun siffofi na idafa[1] kuwa, kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hak'ik'a zuwa ga siffa guda ta hak'ik'a, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda d'aya wacce ake fahimtar irin wad'annan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban.
Amma siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wad'anda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu d'aya, wato kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa[2] ba wajibin samuwa ba, abin da yake nufin kore jiki, da sura, da motsi, da rashin motsi, da nauyi, da rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa. Sannan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa yana daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a k'arshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (s.w.t) kuwa makad'aici ne ta kowace fuska, babu yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawa a hak'ik'aninsa makad'aici sid'if.
Abin mamaki ba zai k'are ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, saboda ya kasa gane cewa siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, sai ya yi tsammanin cewa siffofi tabbatattu suna komawa zuwa korewa ne domin ya samu nutsuwar imani da kad'aitakar zati da rashin k'ididdigarsa, amma sai ya fad'a cikin abin da yake mafi muni saboda sanya ainihin zati wanda shi ne ainihin samuwa, kuma tsantsar samuwa wanda ba shi da wata nakasa ko wata fuska ta siffar yiwuwar samuwa. Sai ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma tsantsar korarre[3], Allah ya kiyaye mu daga tab'ewar wahamce-wahamce da kuma zamewar duga-dugai.
Kamar yadda mamaki ba ya k'arewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- k'ari ne a kan zatinSa, ya yi imani da k'ididdigar zatin Allah wajibin samuwa, da samuwar ababan tarayya[4] gareshi, ko kuma wannan magana tasa ta kai shi ga imani da hauhawar zatinsa mad'aukaki.
Shugabanmu Amirul Muminin (a.s) ya ce:
Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[5], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wad'ancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya k'ididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[6].
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Fassarar Littafin Muzaffar
[1] - Siffofin Idafa su ne siffofin da suke nuna alak'a tsakanin bangare biyu, wato bangaren Allah da kuma na bayinsa, kamar arzutawa da halittawa.
[2] - Shi ne wanda samuwarsa daga waninsa take wato shi abin halitta ne.
[3] - Wannan ra’ayi ne na d'aya daga malaman mu’utazila da mabiyansa, abin da yake nufi shi ne, siffofin tabbatar da kamala ga Allah suna komawa ga kore tawaya ne, kamar idan aka ce mai iko ne to awajansu abin da ake nufi shi ne ba gajiyye ba ne, amma wai ba a iya cewa ma’anar ta mai iko ne, domin gudun kada a kamanta shi da bayinsa. A lokacin da wannan ra’ayi ya kai su ga tauye Allah (s.w.t) domin idan aka ce mai ilimi yana nufin ba jahili ba amma kuma ba ya nufin ma’anar mai ilimi, wannan a gun mu mazhabar imamiyya isna ashariyya tauye Allah ne da kore masa kamala, Allah ya tsare mu daga kaucewar tunani.
[4]- Wannan ra’ayi ne na Ash’ariyya da suke ganin siffofin ma’ani ba kawai ma’ana ba ne da Allah shi ne hak'ik'anisnsu na zahiri kamar yadda sauran siffofinsa suke, suna ganin wad'annan siffofi suna da tabbatattun hak'ik'aninsu a zahiri na hak'ik'a da suke siffantuwa da su, misali kamar Ali da yake da sunaye ne da siffofi, da za a ce masa Ali d'an Muhammad, baban Isa, dogo ne, kuma kakkaura, sai a ce siffofinsa d'an Muhammad, baban Isa, da dogo, da kakkaura, duk a zahiri suna da d'aid'aikun da suke siffantuwa da su, sai ya zama Ali shi yana nuni izuwa gareshi ne kawai banda sauran siffofi, sauran siffofi kuwa suna da nasu samammu na zahiri da suke siffantuwa da su. Da maganar Ash’ariyya gaskiya ne da a nan Allah ya zama guda takwas, kamar yadda a misalinmu Ali zai zama su biyar, wato Ali, da d'an Muhammad, da baban Isa, da dogo, da kuma kakkaura.
[5] - Wato siffofn k'ari guda bakwai da masu wannan nazari suka ce su ba Allah ba ne amma sun dad'u ga zatin Allah kuma zatin yana buk'atarsu a ra’ayin Ash’ariyya kamar yadda ya gabata a bayaninmu, da kuma Siffofin khabariyya; kamar hannun Allah, da idonsa, da fuskarsa, da suke da tawili da ma’anar da laraba suka sani alokacin saukra da littafin kur’ani mai girma, Sifffofin khabariyya siffofi ne wadanda ake tawilinsu kamar tawilin hannu da k'arfi ko iko ko alk'awarin Allah, kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a kur'ani mai girma.
[6] - Alhalin Allah yana ko'ina bai keb'anta da wani wuri ba.
Ƙara sabon ra'ayi