Ubangiji Madaukaki

Allah Ubangiji Madaukaki
Allah Madaukaki daya ne makadaici babu wani abu kamarsa, magabaci ne bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jauhar[1] ba ne kuma ba ard[2] ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi. Gannai ba sa riskarSa Shi kuwa yana riskar gannai.
Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (a.s), mamakin kyawun wannan bayani mai hikima! Mamakin wannan abin nema na ilimi mai zurfi!` .
Haka nan ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar kiyama a cikin kafirai[3] koda kuwa ya kore masa kamantuwa da jiki, batun baka ne kawai, kuma irin masu wannan da’awa sun sandare ne a kan zahirin laffuzan Kur’ani ko hadisai, kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su, suka kuma kasa yin amfani da aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai da ka’idojin aron kalma, da kuma ka’idojin aron ma’anar kalma suke.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

[1] - Abin da yake bai damfara ko dogara da wuri ba.
[2] - Abin da yake ya damfara ko ya dogara da wuri.
[3] - Karfici a nan ba irin wanda yake fitar da mutum daga musulunci ba ne kamar yadda yake sananne cewa kafirci matakai-matakai ne.

Ƙara sabon ra'ayi