Sakon Ta'aziyyar Imam Khamenei Biyo Bayan Hatsarin Da Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mahajjata Da Dama
Sakamakon hatsarin da ya faru a Mina a yau din nan da yayi sanadiyyar rasuwar wani adadi mai yawa na mahajjatan Dakin Allah da suka fito daga kasashen duniya daban-daban, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta'aziyyarsa, inda yayin da yake nuna damuwarsa kan wannan lamari da kuma taya wadanda abin ya ritsa da su juyayi, ya jaddada cewar: Wajibi ne gwamnatin Saudiyya ta amince da gagarumin nauyin da ke wuyan dangane da wannan babban musiba mai sosa rai, sannan kuma ta sauke nauyin da ke wuyanta cikin gaskiya da adalci.
Haka nan kuma yayin da yake sanar da zaman makoki na kwanaki uku a duk fadin kasar Iran saboda wannan musiba da ta faru, Jagoran ya bayyana cewar: Sannan kuma bai kamata a rufe ido kan mummunan tsarin gudanarwa da kuma matakan da aka dauka wadanda ba su dace ba, wadanda su ne ummul aba'isin faruwar wannan lamari.
Abin da ke biye fassarar sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci ne:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Lalle Daga Allah Mu Ke, Kuma Lalle Ne Mu, Zuwa Gare Shi, Mu Ke Komawa
Lalle babbar musibar da ta faru a yau din nan a Mina wadda ta yi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na Bakin Ubangiji da Muminai masu hijira zuwa ga Allah da suka fito daga kasashen daban-daban ya haifar da alhini da bakin ciki mai girman gaske a duk fadin duniyar musulmi sannan kuma ya mayar musu da idinsu ya zamanto juyayi da zaman makoki. A kasar mu ma wani adadi mai yawa na iyalai wadanda cikin shauki da kauna suke jiran dawowar ‘yan'uwansu alhazai, amma a halin yanzu suna cikin juyayi da zaman makokinsu. Ni din nan cikin tsananin bakin cikin da taya wadanda abin ya shafa juyayi na ke isar da ta'aziyya da juyayi na ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) haka nan ga Waliyullahil A'azam mai girma Sahib al-Zaman (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) wanda shi ne ma'abocin wannan juyayi na asali, haka nan ga dukkanin wadanda suke cikin juyayi a duk fadin duniyar musulmi musamman wadanda suke cikin Iran. Ina rokon rahamar Allah Madaukakin Sarki, mai gafara da jin kai ga wadannan bakin Allah (da suka rasa rayukansu) da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka sami raunuka.
A nan ya kamata in yi ishara da wasu abubuwa kamar haka:
1. Ina kiran jami'an ofishina (da ke Saudiyya) da hukumar aikin hajj da su yi aiki tukuru wajen gano wadanda suka rasa rayukansu da kuma kula da ba da magani ga wadanda suka samu raunuka da dawo da su gida sannan kuma su ci gaba da aiko da labaran abin da ke faruwa kamar yadda suke ci gaba da yi. Sannan kuma dukkanin wadanda suke da karfi da damar taimako, to su taimaka musu.
2. A yi dukkanin abin da za a iya wajen taimakon sauran alhazan da suka fito daga sauran kasashen duniya da kuma sauke nauyi na ‘yan'uwantaka ta Musulunci.
3. Wajibi ne gwamnatin Saudiyya ta amince da gagarumin nauyin da ke wuyanta dangane da wannan babban musiba mai sosa rai, sannan kuma ta sauke wannan nauyin cikin gaskiya da adalci. Haka nan kuma bai kamata a rufe ido kan mummunan tsarin gudanarwa da kuma matakan da aka dauka wadanda ba su dace ba, wadanda su ne ummul aba'isin faruwar wannan musiba.
4. Da yardar Allah wadanda suka rasa rayukansu yayin wannan hatsari suna cikin wannan kalami mai haskakawa na Alkur'ani mai girma da ke cewa: "Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, ladarsa tana wajen Allah" (Suratun Nisa' 4:100) Lalle wannan babban abin kwantar da hankali ne ga wadanda suka bari. Wadannan mutanen sun koma ga Mahaliccinsu ne bayan dawafi da Sa'ayi sannan kuma bayan sa'oi masu albarka na Arafa da Mash'ar sannan kuma a daidai lokacin da suke aiwatar da aikin hajji ne. Insha Allah za su kasance cikin rahama da tausayawar Ubangiji.
A saboda haka a daidai lokacin da nake sake mika sakon ta'aziyya da juyayi na ga wadanda suke cikin halin juyayi, ina sanar da zaman makoki na kwanaki uku a duk fadin kasar nan (Iran).
Amincin Allah ta tabbata ga bayin Allah Salihai.
Sayyid Ali Khamenei
02, Mehr, 1394
(24, Satumba, 2015)
Ƙara sabon ra'ayi